IQNA

Hizbullah Ta Mayar Da Kakkausan Martani Kan  Al Saud

15:49 - October 29, 2021
Lambar Labari: 3486489
Tehran (IQNA) Hizbullah ta yi kakkausar suka kan matakin da Saudiyya ta dauka na sanya gidauniyar Al-Qard al-Hassan a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta yi kakkausar suka kan matakin da Saudiyya ta dauka na sanya gidauniyar Al-Qard al-Hassan a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

A jiya Alhamis, kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da matakin na gwamnatin Al Saud, inda ta bayyana hakan a matsayin "cin zarafi ga kasar Labanon" da kuma tsoma baki a harkokin kasar  na  cikin gida.

Hezbollah ta jaddada cewa matakin na Saudiyya yana a matsayin kaskantar da kai ne ga gwamnatin Amurka, da kuma hidima ido rufe ga manufofin makiya al’ummar musulmi wato yahudawan sahyoniya.

Ta kara da cewa: Wannan matakin na gwamnatin Al Saud ba zai iya sawa ko hanawa ba, ko kuma kawo wani cikas a cikin aikin wannan cibiyar jin kai ba.

Bayanin na Hizgullah ya ce, wannan cibiya ta sadaukar da kanta da abin da take da shi ne baki daya wajen yi wa al'ummar kasar Lebanon hidima, musamman talakawa da mabukata daga cikinsu, wanda kuma kowa ya san haka a kasar Lebabon.

Gidauniyar Al-Qard Al-Hassan da ke kasar Lebanon karkashin kulawar Hizbullah, ana daukarta a matsayin daya daga cikin cibiyoyi da ke taimakawa al'ummar Lebanon wajen fuskantar matsalar rayuwa da kuma munanan yanayin tattalin arziki da kasar ke fuskanta karkashin takunkumin Amurka.

Ana ganin cewa Hukumomin Saudiyya sun dauki mataki saka wannan cibiya cikin kungiyoyin ta’addanci ne domin dada wa Amurka da kasashen turai da kuma gwamnatin Isra’ila, kamar yadda ta kame wasu daga cikin jagororin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta jefa su kurkuku, domin dada wa Amurka da Isra’ila.

 

4008752

 

captcha